Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Akayi Da Kudaden Da Kasar Switzerland Ta Mayarwa Najeriya A Baya


A shekarun baya lokacin da kasar Switzerland suka dawowa da Najeriya wasu makurden kudade, sunce sun saka kula da kudaden karkashin wata kungiyar mai zaman kanta, wadda aikin ta shine ta tabbatar da cewa anyiwa jama’a aiki da kudaden.

Sai dai ministan kudi na wancan zamani Ngozi Okonjo-Iweala, wadda ta fito tace duk kudaden da aka dawo da su anyi amfani dasu wajen gina hanyoyi da kiwon lafiya da ilimi da ruwa da wutar lantarki. To sai kuma duk yawan wadannan kudade da akace anyi wanann ayyuka dasu talaka bai gani ba, domin matsalolin da aka ambata har yanzu na ciwa al’umma tuwo a kwarya.

A daya bangaren kuma, a karshen wa’adin tsohuwar gwamnatin da ta gabata an dawo da wasu daga cikin ire-iren kudaden, sai dai kuma an karkatar da su zuwa wata hanya ta daban da sunan za ayi aikin tabbatar da tsaro a kasa. Ta hanyar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sai dai gashi yanzu haka ana kan bincike na badakalar da akayi da kudaden.

Marubuci kuma dan gwagwarmayar kare hakkokin bin Adama, kuma Malami a sashen koyon aikin jarida a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Mallam Kabiru Danladi Lawanti, yayi bayani kan wannan lamari, saurari Lawanti cikin sauti.

XS
SM
MD
LG