A cikin shirin samartaka na yau lahadi, mun karkata akalar shirin ne inda muka ji ra'ayoyin wasu iyaye maza da mata dangane da irin bubuwan da suka fi ci masu tuwo a kwarya a harkokin soyayyar 'ya'yan su.
Kamar yadda malama Lami Sumaiya Murtala daga jahar Kano ta bayyana, tarbiyar yara ta canza ba kamar ta da ba. yawancin matasa sun dogara ne akan irin koyarwar da nagaba da su suka koya masu wanda hakan yasa wasu da dama sun lalace domin kuwa magabatan nasu basu nuna masu hanyar kirki.
Ta kara da cewar nunawa yara so wani lokaci kan hana a tsaya tsayin daka domin dora su a hanyar da ta dace, wannan yana nufin ba'a so a bata wa yara rai dan haka sai kaga an rabi da su suna yadda suka ga dama.
Koda shike yaran suna da nasu laifin, domin kuwa idan suka fita waje, abokan da suke cudanya da su ma na taka rawa a rayuwar su da tarbiyar su.
Haka Malam Mustapha Yako ya kara da cewa kin bin tafarki ko koyarwar addini na daya daga cikin dalilan da suka sa ake samun matsala a harkar soyayya.
Ku biyo mu a shafinmu na dandalinvoa/facebook.com domin fadin ra'ayoyin ku.
Ku saurari karin bayani.