Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Obi Da Victor Moses Zasu Taka Rawar Gani A Karawar Super Eagles Da Egypt -Inji Siasia


Babban Koc mai rukon kwarwa Samson Siasia ya ce a shirye shiryen san a samun nasara akan wasan da kungiyar Super Eagles zata buga da Egypt na shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON, zai yi amfani da kwarewa da kuma sanin makamar taka leda irin ta Mikel Obi mai bugawa kungiyar Chelsea wasa da kuma Victor Moses na kungiyar West Ham.

Siasia a hirar sa da mujallar complete sport ya bayyana jin dadin sa musamman akan yadda ‘yan wasan biyu suka jajirce wajan iya murza leda.

Ya ce “Ina matukar alfahari da yadda Mikel Obi ke mayar da hankali akan duk wasan da ya ba muhimmanci, kuma ya amsa kiran da muka yi masa da shirin karawar da zamu yi da kungiyar ‘yan wasan Misira.”

“Victor Moses ma ya tabbatar mana da kasancewar sa, lallai wannan lamari ne mai karfafa gwiwa musamman a lokacin da muke bukatar kwararrun ‘Yan wasan mu domin fafatawa da Egypt”.

"Ya kara da cewa munsan Egypt zasu zo da kwarrarun ‘yan wasan su ne, kuma nasan cewa kwarewar Mikel da Moses kadai zata daidaita lamarin indai muna bukatar samun akalla maki uku gaba da Egypt a Kaduna".

"Wadannan ‘yan wasa biyu kwarraru ne kuma na yi imanin cewa zasu taka rawar gani wajan samun nasara bisan Egypt. Abin da muke bukata kawai shine, mu bada kokari kuma mu hada da addu’a, zamu doke Misira ko shakka babu".

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG