Yau Dandalin VOA ya sami bakuncin Mustapha Na Biriska, jarumi a fannin barkwanci, kuma ya kwashe shekaru goma sha hudu yana harkar film, ya bayyana mana yadda ya sami kansa a cikin harkar film kamar haka;
Tunda maganar ta yanzu yanzu ce, malamin ya ce ya fi fitowa a fannin bada dariya, kuma abubuwan da suka ja hankalin sa lallai suna da yawa, amma mafi muhimmaci a ciki abubuwan shine jan hankalin da manyan 'yan wasa suka yi wa iayye da su guji dora ma 'ya'yan su maza ko mata talla.
Ya kara da cewa hakan yana gurbata rayuwar yaranne, kuma a lokacin babu wani abu da za'a iya nunawa iyayen illolin sa yaran su talla sai ta hanyar nuna masu ta hanyar shirya wasan kwai kwayon da zai fadakar.
Ya bayyana cewa tunda ya fara wasan barkwanci, bai taba kwatantawa a bayan fage ba woto kafin ya shiga filin wasa. Ya ce baiwa ce kawai da Allah ya bashi, dan haka duk inda ya sami kansa zai iya yin wasan barkwancin ba tare da bata lokaci ba domin kuwa abin yakan zo masa ne musamman lokacin da ake bukatar sa.
Daga karshe jarumin ya bayyana cewar wasan da ya fito da shi ana kiransa BABBAN YARO, wanda Falalu Dorayi ya bada umurni, Adamu Zango kuma ya dauki nauyin sa.
A fannin tsegumi kuma, tawagar Dauda Rara ta sauka a Kano jiya bayan wani wasan bikin aure da suka gabatar a Gusau bisa gayyatar gwamnan jahar, Ali Nuhu ya karbi kambi wanda aka dade ana damawa da shi, Adam Zango kuma ya anshi na jarumin shekara, Hafizu Bello kuma, na gwarzo mai bada umurni da aka gudanar a London.