Wani Kyanwar mai suna Corduroy ya shiga littafin tarihi na duniya a matsayin Kyanwan da yafi kowanne tsawon shekaru yanzu a Duniya. Yawanci dai irin wannan dabbobi basa wuce shekaru goma sha biyar suna rayuwa a duniya.
Ashley Reed Okura, shine mutumin da ya mallaki Kyanwar kuma ya rike shi tun yana ‘dan karami, baya ga Corduroy Okura nada wasu kyanwar har bakwai a gidan sa.
Wannan dai shine karo na biyu da wannan Kyanwar ta sami shiga kundin tarihin duniya a matsayin wanda ya fi kowanne jinsin halittarsa yawan shekaru. Shekarar da ta wuce ne aka lura da haka, bayan nan ne jami’an tantance al’amuran shiga littafin tarihi na duniya suka samo wata Kyanwar mai suna Tiffany wadda shekarunta ya kai 27. Bayan mutuwar ta ne dai Couduroy ya sake zama kan matsayin sa.
Okura dai ya bayyana cewa Kyanwar mai shekaru 26 yana nan cikin koshin lafiya da walwala, a baya ne dai ta dan sami ciwon koda amma yanzu ya warke, kuma yana nan yana ta wasan sa irin na Kyanwa a babbar gonar su.
A lokacin da akayi bukin ranar haihuwar sa wato 1 ga watan Agusta ne dai aka sayo masa wani ‘dan karamin farin bera, a cewar mai mai gidan sa tabbas ya ji dadin lashe beran.