Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutane Miliyan 100 Ne Ke Amfani Da Facebook Lite


Kamar yadda aka sani a baya kamfanin Facebook ya canza salon yadda manhajarsa ta wadda aka fi sani da app ta wayoyin hannu masu amfani da manhajar Android, wadda ake kira Facebook Lite, an dai kera wannan manhaja ne domin mutanen da basu da internet mai karfi ko masu kananan waya, kamar mutanen dake kasashe masu tasowa.

Bayan kaddamar da wannan manhaja tun a watan Yuni na shekarar da ta gabata, ita dai wanann app dake aiki kawai a wayoyin dake da manhajar Android tayi girman da ba a saba gani ba inda yanzu haka mutane Miliyan 100 ke anfana, yawan mutanen da aka samu masu amfani da ita yanzu haka ya haura yawan mutanen da ke amfani da tsohuwar manhajar waya da Facebook ya fitar da farko.

Kamar yadda Facebook yace wannan app dana farin jinni a kasar Brazil da india da Indonesia da Mexico da Philippines, duk da haka kuma app din na amfani da yarukan duniya har 56, kuma yanzu haka kasashen duniya 150 na amfani da su.

Ita dai wannan app bata da wani nauyin da zai kasa sauke wata makalar da ake son a sauke, domin girmanta baifi megabit 1 ba kamar yadda aka bayyana. Tana kuma aiki ne cikin sauki ba tare da wani sarkakiya ba, amma yanzu Facebook na kara mata wasu fasali wanda suka hada da hotan bidiyo da daura hotuna masu yawa da karawa hoto girma a yayin da aka taba shi.

Facebook dai yayi kokari wajen kirkirar wannan app dake aiki a wayoyi masu manhajar Android. Babu masaniya kan ko yaushe kamfanin zai fitar da irin wannan manhaja da zata ke aiki a manhajar ios irin ta wayar iphone.

XS
SM
MD
LG