Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'ar Dogaro Da Kai Ko Babu Aikin Gwamnati Hakar Ka Na Cimma Ruwa


Na koyawa ‘ya ta mai shekaru 11 yadda ake sana’ar hannu inda take taimaka min wajen yin ‘Ambar da man shawafa Basilin domin ta zama mai dogaro da kai a nan gaba inji malama Hussaina Shu'ibu Arab.

Ta bayyanawa wakliliyar DandalinVOA hakan ne tare da karin haskebisa dalilan da suka karfafa mata gwiwa bayan ta kammala karatunta shekaru uku da suka gabata kuma aiki ya gagare ta hakan yasa sa ta fara sana’ar hannu.

Hussaina ta ce tun da ta fara wannan sana’a sai dai ta ce san barka domin kuwa sana’ar dogaro da kai ta huce mata takaici.

Malama Hussaina ta ce kawo yanzu takan samu kwangilar yin sabulu, ambar na mata man shafawa da sauransu wanda a cewarta ko bata samu aikin gwamnati ba hakar ta ta cimma ruwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG