Sana’ar gwari kan taimakawa matasa domin samun hanyar da zasu nufi rayuwa da kawar musu da hanyar shiga wani hali ko damuwa, Dandalin VOA ya zanta da wani matashin yaro wanda yake sana’ar gwari inda yake sayar da Lemo, Ayaba, Kankana da Gwanda da sauran kayayyakin gwari.
Matashin dai yace ya fara wannan sana’a shekaru biyu kenan da suka gabata, ya dai fara yin tane domin taimakawa kansa wajen neman ilimin boko, a kasancewar ba’a saka shi makaranta a gidan su ba tun farko amma da yayi wayo ya fara gane amfanin ilimin boko, sai ya maida kansa makaranta inda ya fara da shiga makarantar firamare, wanda a yanzu haka yana aji uku.
Yace wannan sana’ar da yake ta gwari yana taimakawa kansa ne da kuma mahaifinsa, yana dai yin sana’ar sa bayan ya dawo daga makaranta. Burin wannan matashi dai shine ya iya rubutu da karatu, wanda yake fata idan ya sami ilimin boko ya kuma samu aikin yi, idan hakan bata samu ba zai cigaba ne da sana’ar sa ta gwari.