Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'ar Sabulu ta Samar Min da Kayan 'Daki


Wata kasuwa a Maiduguri, Nijeriya
Wata kasuwa a Maiduguri, Nijeriya

A rohoton Dandalin VOA na matasa masu dogaro dakai na fannin illmi, zamantakewa dama siyasa. A yau wakilayar Dandalin VOA ta zanta da wata mata mai kamar maza, wadda tayi fice a sana’ar sabulun wanke wanke na ruwa.

Malama Lubabatu Abubakar dai tace ta fara wannan sana’ar tata bayan ta kammala karatunta na gaba da sakandare, inda tace tana sana’ar ne domin tazamo mai dogaro da kai, tace da sana’ar dai ta yiwa kanta kayan ‘daki.

Ata bakin Lubabatu, tace tana yin sana’ar sabulu wanda akeyi a gida, kuma tana wannan sana’ar ne domin kashe wa kanta bukatu na yau da kullum, da kuma taimakawa iyayen ta.

Tace akwai alfanu a tare da wannnan sana’a kasancewar zakasa jari kadan, don jarinta bashi da wani yawa amma da sa albarkar Allah sai aga an sami riba mai yawa a cikin ta, idan har kayi sabulu yin farko, a missali an kashe Naira dubu biyar to akalla ba akasara ba za’a samu wajen Naira dubu goma sha biyar.

Tace tana amfani da ribar ta wajen daukewa iyayenta nauyi tun ma kafin tayi aure. Saurari hirar da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir da Malama Lubabatu Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG