Hassan Gimba Ahmed wani kwararren dan jarida ne dake babban birnin tarayya mai yin sharhi kan al’amurran yau da kullum, kuma yana kallon yadda gwamnatin tarayya ta ce zata yi amfani da kudin tallafain mai domin samar wa matasa sana’oi ta fuskoki biyu.
A cewar sa, “gwamnatoci sun dade suna yi wa mutane alkawari amma ba’a gani a kasa, ita wannan gwamnatin tana da abu biyu dake tattare da ita, na farko ba’a taba yin gwamnatin da jama’a suka yarda da ita kamar wannan ba domin ana ganin cewar shugaban ta Muhammadu Buhari mai gaskiya ne da rukon amana, na biyu kuma ba’a taba gwamnatin da jama’a suka sawa uzuri kamar ta ba.
“Wannan ya kasance a sakamakon hangen alherin da sukai wa gwamnatin ne , dan haka kamar yadda aka hakura aka bada uzuri har aka shekara guda, yanzu ne kwanakin da gwamnatin ta fito ta ce an fara, tunda an sama budget hannu. Dan haka idan aka bata lokaci zuwa karshen shekarar nan lallai za’a gane irin kamin ludayin ta.”
Tuni ‘yan Najeriya ke ci gaba da bayyana ra’ayoyi masu cin karo da juna kamar yadda Malam Sabo Imamu Gashuwa ya ce a ganin sa duk muradun da gwamnatin ta rubuta a takarda lallai suna da matukar kyau amma ba lallai ne ta aiwatar da su ba saboda watanni goma Kenan har yau ba labara har jama’a sun kaiga kokawa.
Shi kuma Sale rabi’u cewa ya yi a nasa ra’ayin, tallafawa matasa da kudin tallfin mai zai yi matukar amfani amma fa sai dai idan gwamnati zata cika alkawari kamar yadda ya kamata domin kuwa an dade ana ruwa kasa na shanye wa.
Ga cikakken rahoton.