Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaicin Na’urorin Zamani Kan Kai Mutum Ga Wani Hali


FILE - An employee works at the headquarters of Kaspersky Labs, a computer security company in Moscow.
FILE - An employee works at the headquarters of Kaspersky Labs, a computer security company in Moscow.

Wani mutum ‘dan Amurka mai suna Lucas Hinch mai shekaru 37 da haihuwa, ya harbi kwamfutar sa har sau takwas lamarin da yasa jami’an tsaro suka bashi takardar zuwa gaban kuliya domin amsa laifinsa.

Jami’in ‘yan sanda mai suna Jeff Strossner yace, mutumin mai suna Lucas Hinch ya fada masa cewa ya dade yana fada da na’ura mai kwakwalwa da ya mallaka, a dalilin rashin aiki yadda ya kamata kuma da takaicin kasa gyara ta, daga karshe dai ta kai shi bango inda ya ‘dauko komputar zuwa bayan gidansa ya kuma bude mata wuta da bindigarsa da harbi har takwas a kokarinsa na kashe ta.

An dai jami’an tsaro sun same shi da aikata laifin harba bindiga a cikin gari, amma ata bakin Lucas bashi da masaniyar laifi ne mutum ya harbi komfutar sa a bayan gidan sa, alkaline dai zai yanke hukuncin daya kamaci laifin.

XS
SM
MD
LG