Matsalar wutar lantarki a wasu kasashen Afirka ta zama tamkar ruwan dare, wadda hakan ke zama wata matsala ga rayuwar al’umma har ma da lafiyar su.
Ga duk wanda ya ziyarci Asibitoci a Najeriya, musammam ma karkara ba koda yaushe ake samun wutar lantarki ba, wani lokacin ma wutar na ‘daukewa alokacin da likita ke tsakiyar yiwa maras lafiya aiki. Abin takaici ma anan shine yadda za’a ga malaman jinya na amfani da fitilar kwai domin duba marasa lafiya cikin dare ko lokacin da aka dauke wuta.
Ana fuskantar ire-iren wannan matsala a Najeriya dama sauran kasashen Afirka, kuma mutane da yawa na rasa rayukansu.
Dalilin hakane wata ‘yar Najeriya mai suna Louise Jaiyeola Oduyoye, mai shekaru 21 da haihuwa kuma ‘daliba a jami’ar Derby dake Birtaniya, ta kirkiri wani batirin tafi da gidan ka mai suna Neva da zai taimaka likitoci don kammala aikin su alokacin da aka fuskanci matsalar ‘dauke wuta a yayin da ke cikin aikin tiyata, da zarar an dauke wuta batirin zai ci gaba da baiwa na’urorin dakin karfin wutar da za’a iya kammala duk aikin da akeyi alokacin.
Louise dai ta kirkiri wannan fasaha ne domin taimakawa kasashen da ke fama da rashin wuta, domin su samu yin aiki cikin kwanciyar hankali da kaucewa tafiya zuwa Asibitocin kasashen waje. Wannan kirkira tazo ne alokacin da ya kamata, kuma burinta shine ta samar wa da Asibitoci a fadin nahiyar Afirka wannan Batiri mai suna Neva.