Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Raba Wasu Takardun Dake Barazanar Kada Mutane Su Fito Zabe


Shugaban kungiyar Boko Haram
Shugaban kungiyar Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun afkawa jami’an tsaro a Gombe kafin daga bisani suka fice daga garin, suka ma koma inda suka fito a jihar Borno, harma suka rabawa mutane wasu takardu suna yiwa jama’a kashedi cewar kada su fita suyi zabe.

Dakta Bawa Abdullahi Wasai wani masanin harkar tsaro ne a Najeriya, yace, “har mutane suzo a cikin layi na motoci su wuce ba daya ba biyu ba, wannan hari kuma da ake kaiwa a wannan jiha ba daya ba biyu ba to wanene mahaukaci? Abinda zance kawai shine ana yaki da sojan gona a kan kasa da al’umma da basu jiba da basu gani ba. Amma indai mutanen nan zasu shiga cikin motoci, kuma suzo suci karensu ba babbaka, harma su dauki gawarwakin mutanensu da aka kashe to akwai wata kullalliya.”

Shima mallam Habu Bawa na kungiyar fafutukar tabbatar da shugabanci na gari a kasar, yace dole ‘yan kasar suyi karatun ta nutsu game da abubuwan dake faruwa a yanzu.

Ahmed Lawan, kusa ne a jam’iyyar APC a jihar Adamawa, nama ganin jama’a zasu jajirce duk kuwa da abin da ya kira barazanar da ake yi, kuma wannan wayone akeyi saboda a hana zabe. Yakuma yi kira ga jama’a da su fito suyi zaben su, saboda duk wata barazanar su bazata baiwa mutane tsoro ba. Harma ya roki gwamnati data bari ayi zabe domin shi zai karawa kasa mutunci a duniya.

Shikuma a martanin da ya bayar shugaban cibiyar bayar da bayanai akan ayyukan ta’addanci a Najeriya, mista Mike Omeri yace ba haka abin yake ba. Inda yace, “za’ayi kokarin a rage afkuwar irin wannan harin da ake kaiwa jama’a a tabbatar kuma duk wuraren da suke zama a hannun ‘yan Boko Haram din an kwato su daga wurin su.” Ya cigaba da cewar yana daga cikin dalilan dayasa sojoji suka bada shawarar dage zaben, domin abin da sojoji suka sani mutane basu sani ba.

Saurari cikakken rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

XS
SM
MD
LG