Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata Dalibai Su 44 Ne Suka Tsere Ya Zuwa Yanzu - 19/4/2014

Wasu mutane kennan daga Gwoza, jihar Borno, da tashe-tashen hankula ya raba da gidajensu, suna taro a sansanin ‘yan gudun hijira a lokacin da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima (babu hotonshi) a garin Mararaba Madagali, jihar Adamawa. Fabrairu 18, 2014.

Jami'ai a Najeriya sun ce adadin dalibai mata 'yan sakandare da suka tsere daga hannun wadanda suka sace a wata makarantar sakandare a Jihar Borno, ya karu zuwa 44.

Kwamishinan ilmi na Jihar Borno, Inuwa Kubo, ya fada yau asabar cewa har yanzu akwai dalibai 85 da ba a gano ba, a bayan da 'yan bindiga suka abka makarantar sakandaren garin Chibok a arewa maso gabashin Najeriya ranar litinin suka sace dalibai 129.

A ranar jumma'a, shugabar makarantar, Asabe Kwanbura, ta ce wasu daga cikin daliban sun tsere ta hanyar yin tsalle kasa daga cikin motar da aka tara su, yayin da wasu kuma suka samu sukunin tserewa daga sansanin da aka kai su cikin daji.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce tana neman inda daliban suke. Haka kuma hukumomi sun ce mafarauta da 'yan banga su na taimakawa wajen neman wadannan dalibai mata a cikin dajin Sambisa, inda aka yi imanin 'yan Boko Haram sun buya.
XS
SM
MD
LG