Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Masu Fama Da Talauci A Duniya Ya Zarce Yadda Bankin Duniya Yake Kiyasi - 11/4/2014


Wani sabon bincike ya nuna cewa watakila yawan masu fama da talauci a duniya ya zarce yadda ake kiyasi da kimanin sulusi guda, watau kashi 1 cikin uku. Ana bayyana talauci a zaman mutumin dake rayuwa a kan kudi kasa da naira 200 a rana, a bisa alkaluman bankin duniya.

Ana amfani da wadannan alkaluma na bankin duniya sosai a zaman ginshikin bullo da dabarun yaki da talauci a duniya. Amma masu sukar lamiri sun ce kayyade mai fama da talauci a zaman wanda ke rayuwa kan kasa da Naira 200 a rana, ba daidai ba ne domin kuwa hakan bai yi la’akari da dukkan bukatun bil Adama na yau da kullum ba.

Masu bincike a jami’ar Bristol sun duba mafaka, samar da wurin bahaya, ruwan sha, abinci mai gina jiki, kiwon lafiya, ilmi a tsakanin mazauna tsibirin Vanuatu a tekun Pacific.

Abubuwan da suka gano sun nuna cewa alkaluman na bankin duniya ba su wadatar ba wajen auna talauci.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:44 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG