Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Borno, Yobe da Adamawa Sun Ce Ba Su Yarda A Sake Sabunta Dokar-Ta-Baci A Jihohinsu Ba - 10/4/2014


Taswirara jihohin da aka kafa dokar-ta-baci
Taswirara jihohin da aka kafa dokar-ta-baci
Gwamnonin jihohin Borno da Yobe da Adamawa sun gudanar da taron koli domin nazarin dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta kafa a jihohinsu, da kuma matakan da suka kamata a dauka na shawo kan dalilan da suka janyo kafa dokar ta bacin.

A karshen taron dai, gwamnonin sun amince da cewa ba su yarda da a sake sabunta dokar ta bacin ba.

Haka kuma, su na son a dauki sabons alo na shawo kan wannan matsala tun da shekara guda ke nan ana aiki da dokar ta baci ba tare da an samu nasarar shawo kan matsalar ba, sai ma abubuwan da suka kara yin muni.

Wannan yana zuwa yayin da wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta ziyarci yankin, ta kuma ce lallai akwai abin dubawa kan yadda har 'yan Boko Haram suke iya kai hari su yi awoyi biyar cikin gari ba tare da hukuma ta bis awunsu ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:44 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG