Wasu rahotannin dake fitowa daga garin Mubi na Jihar Adamawa, wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace, na cewa sabbin masu iko da wannan gari sun fara aurar da duk wata yarinyar da shekarunta na haihuwa ya kai 10.
Rahotannin suka ce har su ma matan auren da mazajensu suka bar wannan gari domin tserewa daga 'yan bindigar na Boko Haram, ana tilasta musu a kan cewa lallai su sake yin wani auren.
Wannan yana zuwa a yayin da wasu 'yan jihar Adamawa ke yin kira ga manyan jami'an gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan 'yan asalin yankunan da suka fada hannun Boko Haram, da su yi murabus daga gwamnatin domin nuna rashin jin dadin rikon sakainar kashin da gwamnati ke yi ma wannan lamarin.
Your browser doesn’t support HTML5