WASHINGTON, DC —
Wata sabuwar fitina ta barke a garin Wukarin Jihar Taraba a tsakanin Hausawa da Fulani a gefe guda, da kuma ‘yan kabilar Jukun a daya gefen, har an yi hasarar rayuka da dama.
Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya zanta da wasu mutanen, wadanda su na cikin magana da su ma aka fara jin karar harbe-harbe.
Daga yankin kudu maso yammacin Najeriya kuma, al’ummar Arewacin Najeriya dake Oyo, sun rungumi wani sabon aikin gayya domin taimakawa kai da kai, kamar yadda wakilinmu Hassan Umar Tambuwal ya gano a wata makabarta dake Ibadan, wadda Mai Martaba Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, ya saya don amfanin 'yan arewa.
Your browser doesn’t support HTML5