Karshenta dai, kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth ta samu hayewa zuwa ga wasannin Firimiya Lig na Ingila a karon farko a tarihinta, a matsayinta na zakarar wasannin Lig-Lig rukuni na biyu na Ingila, kuma a bayanda kungiyar Watford ta watsar da wannan kambi ana saura kasa da minti daya a tashi daga wasa yau asabar.
Kungiyar Watford, wadda tun farko ta samu garanti cewa zata shiga wasannin Firimiya Lig, ita ce a saman teburin Lig-Lig rukuni na 2 na Ingila ya zuwa karawarta da Sheffield Wednesday yau asabar, kuma tana ba Sheffield kashi da ci daya da babu, kafin tayi sako sako, ‘yan Sheffield suka rama wannan ci aka tashi kunnen doki.
Wannan ya ba Bournemouth sukunin lashe rukuni na biyu na wasannin lig-lig na Ingila da maki daya a bayan da ta doke Charlton da ci 3-0, shekaru biyar kacal a bayan da ta tsamo kanta daga rukuni na 4 na wasannin lig-lig na Ingila.
Har yanzu akwai gurbi guda daya da ya rage ga kungiyar da zata samu nasara a tsakanin sauran kungiyoyi 4 dake bi baya a rukunin lig na 2 din, inda Norwich da Ipswich zasu kara yayin da Middlesborough da Brentford su ma zasu kece raini.