Berlusconi Yana Tattauna Sayar Da Kulob Din AC Milan

Mai koyar da wasa na AC Milan, Massimiliano Allegri.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Silvio Berlusconi, wanda tsohon firayim ministan Italiya ne, yace watakila zai ci gaba da rike fiye da rabin jarin wannan kulob da ya shafe kusan shekaru 30 yana mallakarta, a furucinsa na farko game da yiwuwar sayar da ita.

A yau asabar Berlusconi ya gana da wani dan kasuwar Thailand mai suna Bee Taechaubol a hotel din dan kasuwar dake tsakiyar birnin Milan domin ci gaba da tattaunawa kan sayarda kulob din.

An sa ran cewa Taechaubol da abokan huldar kasuwancinsa zasu sayi kasha 51 zuwa 60 cikin 100 na jarin kulob din AC Milan, amma Berlusconi yace ana tattaunawa a kan komai, kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da rike kasha 51 cikin 100 na jarin kulob din.

Berlusconi, wanda sau uku yana zama firayim ministan Italiya, ya karbi ragamar shugabancin AC Milan a watan Fabrairun 1986, ya kuma jagoranci lokutan da kulob din ta fi yin suna da samun nasarori.

Berlusconi, mai shekaru 78 da haihuwa yace zai ci gaba da rike mukaminsa na shugaban kulob din.