Kamfanin yin akwatin Samsonite, yana hada kai da kamfanin Samsung domin kera akwati mai kwakwalwa.
Jaridar Daily mail ta ruwaito cewa kamfanonin biyu suna kokarin yin akwatin da mai shi zai iya sanin inda yake a koyaushe, ko daga ina a duniya, zai iya fadawa mutum idan wani ya bude bai sani ba, zai kuma iya yin yawo da kansa.
Shugaban kamfanin Samsonite, Ramesh Tainwala, yace akwatin mai kwakwalwa za a iya sanin inda yake a koda yaushe ta hanyar dubawa a jikin wata manhaja, ko APP, a wayar mutum. Ma’ana idan mutum ya sauka daga jirgi a misali bai ga akwatinsa ba, yana iya dubawa ya ga ko an taho da akwatin ko an bar shi a wani wuri. Akwatin zai iya aikawa da mai shi sako a duk lokacin da aka fitar da shi daga cikin jirgi ko aka bude mai shi bai sani ba.
Amma babban abinda kamfanonin na Samsonite da Samsung suke shirin yi, shine hada akwati mai kwakwalwa wanda zai iya bin mutum da kansa idan ga misali ya doshi filin jirgin sama, ma’ana ba sai mutum yayi ta jan akwati ba, musamman idan akwatunan suna da yawa. Wannan sabon akwatin, zai iya bin mutum a baya duk inda yayi zai bi shi.
Wani kamfani mai suna Bluesmart ma, yana aikin kera akwati mai kwakwalwa, har ma yayi nisa da wannan.