Sha'awa ce Ta Ja Shiga Harka Fina Finai

Garzali Miko

A shirinmu na nishadi a yau mun sami zantawa da Garzali Miko mai komai da ruwanka wanda ya kwashe shekaru goma a wannan harka ta fina finai.

A cewarsa yana shirya fina-finai yana kuma fitowa a matsayin jarumi, ya ce ya fara ne da matsayin mai bada hasake daga bisani ne ya zama mai bada umarni inda a yanzu haka har ta kai ga ya kai matsayin mai shiryawa .

Ya ce sha'awa ce ta ja shi ga harka fina finai inda ya fara tun daga tushe har kawo matsayin da ya tsinci kansa na jarumi a Kannywood.

Yana mai cewa Kalubale a harkar rayuwa duk abinda dan Adam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.