Amurka tayi alkawarin bada bayanai a fili dangane da amfani da jiragen da basu amfani da matuka da take yi da wani lokaci yake da sarkakiya, wajen kai hare kan ‘yan ta’adda.
Mai ba fadar White House shawarwari kan dakile ayyukan ta’addanci Lisa Monaco ta sanar jiya Litinin cewa, gwamnati zata fitar da rahoto kan adadin sojoji da kuma farin kaya da suka mutu sakamakon hare haren jiragen da basu amfani da matuka da kuma wadansu ayyukan yaki da ta’addanci tun daga shekara ta dubu biyu da tara.
Jami’ai sun ce rahoton zai hada da hare haren jirage da basu amfani da matuka, da dakile ayyukan ta’addanci a Iraq, Syria da kuma Afghanistan, wadanda duka ake dauka a matsayin wanda aka kai a wuraren da ake fama da tashin hankali.
Kakakin fadar White House Josh Earnest ya shaidawa manema labarai cewa, za a fitar da bayanan bisa tsarin shugaba Obama na gudanar da komi a bude.
Jami’an Amurka sun ce wannan shirin zai bada damar buga rahoton hare haren da aka kai da jirage da basu amfani da matuki da kuma sauran ayyukan yaki da ta’addanci shekara shekara.