Wani Sojan Amurka Ya Taimakawa 'Yar Najeriya Da 'Ya'Yanta Uku Daga Konewa

Wani Sojan sama dan kasar Amurka, mai suna Daniel Raimondo da taimakon wasu mutane sun taimakawa wata ‘yar Najeriya, Precious Enyioko, dake kasar Koriya ta Kudu a daidai lokacin da gidan da take zaune a ciki ya kama da wuta.

Precious dai na da ‘ya’ya uku masu shekaru hudu da uku da kuma daya suna tare da ita a gidan su bene Kuma su suna hawa na hudu ne kuma gashi ginin ya kama da wuta amma da taimakon wadannan mutane ta jeho yaran ta taga inda wadannan mutane da taimakon barguna suka tare su.

Precious, 'yar shekaru 30, da haihuwa, da farko ta ki jeho yaran kasa tana wasiwasi da roko da ban baki na Sojan yasa daga baya ta amince ta sako yaran kasa ta taga, bayan da ta sako yaran sai itama ta fado kan bargunan dake kasa amma an sa mata katifu a lokacin da Precious, ta duro kasa daga hawa na hudu.

Abin farin ciki shinePrecious da 'ya'yan ta suna lafiya babu wanda ya ji rauni,

, Sajan da ya jagoranci wannan gagarumi taimako yace hayakin da ya gani ya ja hanlainsa zuwa wuri Kuma sai Allah yasa akwai masu bukatar taimako, da Kuma taimakon sauran jama'a aka cimma nasara.

Shi kuwa mahaifin yaran Kuma mijin Precious cewa yayi bai san irin godiyar da zai yi ba yayi mamakin ganin dinbin jama'a da suka taro domin taimakon iyalinsa.