WASHINGTON, DC —
Kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles, gobe zata kara da kasar Burundi, a babban birnin kasar Bujumbura, ranar Asabar 21, ga wannan watan na Mayu, a wani yunjurin kare kambin zakarun ‘yan kasa da masu shekaru ashirin.
A wasanta na farko Burundi, ta sami nasarar kwab daya saboda rashin halartar kasar Congo.
Koch din na Flying Eagles, Emmanuel Amuneke, ya kwashe yawanchi ‘yan wasan da suka bugawa Najeriya, wasa a kasar chile, a gasar ‘yan kasa da shekaru goma sha bakwai, babu wani dan wasa dake wasa a Najeriya, dukkan su masu wasa a waje ne.kamar su Victor Osimhen, Kelechi Nwakali da Samuel Chwukueze.
Za’a fara wasan ne da kafar daya na rana agogon Najeriya.