Kishiyoyi Sun Karyawa Dan Kishiya Dan Shekaru Biyu Kafa

Rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, ta damke wasu matan aure biyu Zanaib da Hafsatu Musa, wadanda ake zargin su da azabtar da wani yaro da shekaru biyu da haihuwa.

Wadannan mata dai kishiyoyin juna ne shi kuwa yaro dan mijin sune wanda mahaifiyar sa suka rabu da mahaifinsa aka barshi a hannun matan baban, domin kula dashi amma mahaifinsa bai san cewa suna ganawa yaron azabar a bayan idon sa.

Su dai wadannan mata sun ganawa wannan yaro azaba ne har sai da ta kai ga sun karyashi a kafa da hannu.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, DSP, Magaji Majiya, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Da yake tsokaci akai Kwamishinan ‘yan Sandan jihar ta Kano, Abbati Dikko, ya bukaci a tura batun ga sashen bincike na CID, domin gudanar da cikakken bincike.

Matar Kwamishinan Hajiya Aishatu Dikko, wace kuma ita ce shugaban kungiyar matan ‘yan Sanda, masu yaki da cin zarafin yara tace zasu bi Kadin wannan lamari har zai baba ta gani.