Yau ne ranar yaran Afirka, rana ta masamman da majalisar dinkin duniya ta ware domin yi nazari game da halin da yaran Afirka ke cikj masamman ganin cewa yake yake sun adadabi nahiyar.
A jihar Bauchi, asusun talafawa yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF,ta shirya taron bitawa ‘yan jarida domin nusar dasu matsalolin dake shafar yara masamman kuma domin su ja hankalin gwamnatoci da al’umar kasa.
Samuel Kalu, jami’in sadarwa na ofishin asusun kula da yara ta UNICEF, a jihar Bauchi, yace dalilin taron na bana shine domin fadakar da ‘yan jarida akan hakkin yara, domin a cewar sa akwai yara da yake basu zuwa makaranta wasu kuma da dama basu samu abinci da kayayyakin more rayuwa.
Ya kara da cewa asusun na bukatar duk masu ruwa da tsaki su hada hannu da asusun a kokarin da take yi na magance sace sacen yara da kuma yi masu fyade.