Ministan matasa da wasani na Najeriya, Solomon Dalung, ya nemi afuwa daga ‘yan wasan kungiyar Flying Eagles, ‘yan kasa da shekaru 23, da jagororinsu wandanda yanzu haka suke kasar Brazil, domin fafatawa a wasanin Olympics.
Ya nemi afuwa ne bisa rashin dauko su akan lokaci daga Amurka zuwa kasar ta Brazil inda ake gudanar da gasar Olympic, yayin da suka sauka a kasar ta Brazil, bayan ‘yan awoyi ne suka kara da kasar Japan, amma duk da haka Najeriya, ta sami nasara akan Japan inda aka tashi wasan 5 da 4.
A wasan na biyu da kasar Sweden, Allah ya sake baiwa Najeriya, nasara inda ta doke Sweden da ci daya mai banhaushi.
Ministan ya bayyana cewa hakan ba za’a dauki matakin hana afkuwar irin haka nan gaba da cewa Najeriya na mai alfahari dasu.
Your browser doesn’t support HTML5