Dan Wasan Kwallon Kafar Da Yafi Tsada A Duniya

APTOPIX Soccer Euro 2016 France Iceland

Sabon dan wasan kwallon kafar Manchester United, Paul Pogba, dan shekaru 23, kuma dan kasar Faransa ya bayana dalilin dawowarsa Manchester United, daga Juventus.

Ya ce ya dawo Manchester United, ne domin yana bukatar ganin cewa ya daga kofin firimiya lig na kasar Ingila, na wannan shekarar.

Bayan haka kuma Pogba, ya kara da cewa yana sun zama zakaran kwallon kafa na duniya ana gaba, Pogba, dai ya sami nasarar cin kofin kasar Italiya, Serie A, har sau hudu alokacin da yake Juventus.

A yanzu haka Pogba, ya rataba hannu domin bugawa Manchester United, ta mau’la har na tsawon shekaru shida wanda haka ke nuni da cewa Pogba shine dan wasan da yafi kowa tsada a Duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Dan Wasan Kwallon Kafar Da Yafi Tsada A Duniya - 2'37"