Kimanin shekaru biyu ke nan da suka wuce, hukumar binciken sararrin samaniya NASA, ta bayyanar da tsinkewar sadarwa, tsakanin wata na’ura da suka harba cikin sararrin samaniya, tun a shekarar 2006. Yanzu haka sun sake hada hanyar sadarwar.
Wata na’urar set light ce mai suna “Solar Terrestrial Relations Observatories” STEREO-B tun a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2014, wannan na’urar ta samu tangarda, wanda hakan yasa basu sanin mai ake gudanarwa a duniyar rana.
Babban dalilin aika wannan na’urar cikin duniyar rana a cewar hukumar NASA, shine don su kara nazari akan halitar Rana, da yanayi na duniyar sararrin samaniya.
A cikin wani yanayi da aka shiga ne wanda yasa na’urar tai zafi, ya zama sanadiyar katsewar sadarwar a tsakani. Na’urar dai ta taimaka matuka, wajen ganin sun fahimci yadda duniyar rana take. Zasu fara wani gwaji don kara tabbatar da ingancin na’urar kamin cigaba da binciken.