A jiya Alhamis ne wata Tauraruwar ‘dan Adam ta tarwatse lokacin da wata roka da ake aikawa sararin samaniya ta fashe a sansanin da ake sarrafasu. Kamfanin Facebook ne zai yi amfani da Tauraruwar wajen ‘kara karfin yanar gizo a nahiyar Afirka da Facebook ke kokarin yi.
Babu wani mutum da ya sami rauni a lokacin fashewar a sansanin da ake kira Cape Canaveral. Mutanen da ke aiki a gine ginen dake nesa da gurin sunji fashewar, wadda ta faru yayin da ake gwaje gwaje kafin ranar da aka saka za a harba ta, wato gobe Asabar.
Wuta ce ta mamaye rokar mai suna Falcon 9, bakin hayaki kuma ya mamaye sama daga inda take ajiye. Tauraruwar ‘dan Adam din wadda aka kera a kasar Israila, ta fado kasa ne alokacin da rokar ta fashe.
Rashin wannan Roka ba karamin koma baya bane ga kamfanin SpaceX na Amurka da kawayensu, ciki harda hukumar sararin sama da Israila, wadda tace zai ‘dauki har zuwa shekaru uku kafin a sake kera irin ta.
Shugaban Facebook Mark Zuckerberg, wanda yake a Afirka jiya Alhamis, yace yana mai matukar takaici ga rashin wannan Tauraruwar dan Adam, wadda akayi niyyar amfani da ita wajen karfafa yanar gizo a kasashen dake yamma da hamadar Sahara da sauran wasu kasashen da ke lunguna a duniya.