Kowane Dan'Adam Na Bukatar Kimanin Kofi 11, Na Ruwa A Wuni!

Ruwa Abokin Rayuwa

Shan ruwa da ya kai adadin lita biyu, nada matukar muhimanci ga rayuwar dan’adam a kullun. Duk dai da cewar yanayin jikin mutun, da iya irin aikin da yake aikatawa a yini, na kara bayyanar da yawan bukatar da jikin mutun yake da shi na ruwa.

Yana da matukar muhimanci mutun ya sha ruwa da suka kai wannan adadin da ake bukata, don tahaka ne wasu cuttutuka bazasu samu wajen zama a cikin jikin mutun ba, idan mutun na shan ruwa yadda ya kamata a yini.

A duk lokacin da wasu sassan jikin mutun suka bukaci ruwa, musamman idan mutun yayi aikin motsa jiki, to yana da kyau mutun ya inganta jikin shi da wadataccen ruwa masu tsafta.

A wani bincike da wata malamar kiwon lafiya ta gudanar Jessica Fishman, tace akwai bukatar mata su sha ruwa da ya kai kimanin kofi goma sha daya 11, a yini sai ta kara da cewar, abun nufi ba wai mace ta dauki kofi tai ta shan ruwa ba, abun nufi shi ne ta sha ruwa, kana taci wasu nau’o’in abinci da suke dauke da ruwa. Haka maza suma suna da bukatar ruwa a jikin su.

Idan za’a gwada adadin yawan ruwan da mutun ya sha, sai aga cewar ya kai kimanin yawan kofi goma sha dayan da ake magana. Koda kuwa mutun yana jin yunwa, kada ya bari yawan ruwan dake cikin jikin shi ya gaza, adadin da ake bukata mutun ya samu a kowane lokaci.