Dan Sanda A Amurka Ya Ba Yarinya Mai Shekaru 2 Da Haihuwa Tarar Kudi Dala $75

Wani jami’in dan’sanda a kasar Amurka yaba wata yariya mai shekaru biyu da haihuwa tikitin tarar kudi dala $75, a sakamakon kamata da laifin zubar da shara ko bata muhalli a birnin Washington DC.

Mahaifiyar yarinyar mai shekaru 2 da haihuwa da dan’sandan ya ba tikitin tarar Teresa Westover, ta bayyanawa kafar talabijin ta FOX tayi kokarin kiran ofishin dake kula da harkokin jama’a amma da muhalli amma sun ki daga waya.

Cike da mamaki mahaifiyar yarinyar ta ce “abin mamaki dan’sanda ya ba ‘yar karamar yarinya mai shekaru biyu da haihuwa tikiti wai dan ta yarda takarda”,

A cewar mujallar Wasshinton post, jami’in ya ga wata fallen takarda ne kusa da ‘Yar karamar yarinyar da sunanta a rubuce bisa takardar, yayin da ita kuma mahifiyar yarinyar ta bayyana cewa basa zubar da shara a waje.

Jami’in yana kula ne da harkokin tsabtace muhalli a wasu yankunan birnin Washington Dc , inda wasu lunguna da dama suka zama tamkar bola inda jama’a ke jefar da duk abin da suka dama, ma’aikatarkula da harkokin jama’a da tsabtace muhalli ta bayyana cewa alhakin ta ne ta tabbatar da kawo karshen zubar da datti da sabawa doka a ko ina.

Ofishin ya bayyana cewa yana aiki tare da jama’ar unguwar da sauran hukumomin da alhakin ya rataya a wuyansu domin tabbatar da ganin an janye tikitin tarar.