A gobe Laraba ake sa ran kamfanin wayoyi na Apple, zasu kaddamar da sabuwar wayar su, ta wannan shekarar. Ana dai ganin cewar wannan sabuwar wayar, da zasu fitar bata dauke da wasu manhajojin zamani da suka fi na tsofaffin wayoyin su.
Kamfanin dai sun samu raguwar cinikayya a bana, irin yawan wayoyin da suka siyar a shekarar 2014, yana da wuya su sake yin kasuwar da ta kai hakan. Kamfanin ya samu matsalar faduwar hannun jari, da yakai kashi ashirin da uku 23%.
A cewar wani dan kasuwar wayoyi na kasa-da-kasa Mr. Neil Cybart, yana da wuya kamfanin su sake tashi kamar yadda su kayi a baya, yana ganin kimanin nan da shekaru fiyar masu zuwa, baza su sakeyin tasiri sosai ba, wannan wata damace ga abokan hamayyar sun Samsung, su kwace kasuwar matuka.