Lauyan Matashin Danjarida Salkida Da Sojin Nageriya Ke Nema Ruwa A Jallo Ya Yi Korafi

Rahotanni sun bayyana cewa an hana matashin dan jaridar nan Ahmad Salkida, wanda rundunar sojojin Najeriya ta kama a tashar jiragen sama ta kasa da kasa dake Abuja, a ranar litini bayan sa sunansa tare da wasu mutane biyu cikin jerin sunyen mutanen da take nema ruwa a jallo ganawa da lauyan sa.

Salkida wanda ake zargi da alaka ta kusa da kusa da shugabannin kungiyar boko haram, ya fada hannun jami’an tsaron kasar ne a yayin da yake kan hanya domin mika kansa ga rundunar sojin.

Mr Falana fumed, shine lauyan dan jaridar wanda a halin yanzu ake kyautata zaton yana hannun hukuma a ofishin, jami’an ‘yan sandan farin kaya ya bayyana cewa hukumar ta hana shi ganawa da dan jaridar, sai dai ya kara da cewa yana nan yana ci gaba da neman hanyoyin da zai sami damar yin hakan.