Wata mata ta sassare mijinta da adda a yayin da yake cikin barci a sakamakon kishin jin cewa yana neman wata.
Matar mai suna Kemi, wadda ke hannun jami’an ‘yan sanda a jihar Legas ta bayyana cewa ta sayo addar ne sati biyu da suka gabata ta kuma jira lokacin da ya dace domin amfani da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya kwanan biyu yana neman wata mata lamarin da ya fara hana shi zama gida kamar yadda ya saba da a da.
Majiya daga iyalin Kahinde Etu, wanda aka sassare ta bayyana cewa matar ta tunkari mai gidan nata da maganar amma sai ya tayar mata da cewa yana da ‘yancin sake aure kokuma auran matar da yak enema.
Rahotannin sun bayyana cewa Kemi ta shiryawa mai gidan nata abincin da yafi kauna sa’annan ta barshi ya kwanta ya fara barci daga nan ta shigi saran sa da sabuwar addar da ta saya ta boye har sai da ya suma, ana cikin haka ne yaran suka dora kuwwa har saida makwabtan su suka kai dauki inda suka garzaya da Kehinde asibiti a sume kafin daga baya ya farfado.
Wasu daga cikin makwabtan ne suka rike ta har sai da jami’an ‘yan sanda suka bayyana inda suka yi awon gaba da ita. Da farko bata nuna wani dalilin aikata wannan danyen aikin ba, sai data budi baki ta tace wai har mijin nata nada karfin gaban fada mata cewa zai kara aure, ta kuma kara da cewa ta sassare shi ne domin bazata iya barin shi ya auri wata mata ba.