WASHINGTON D.C —
Wani matashi mai bautar kasa (NYSC) mai suna Dayo ya gamu da ajalinsa a wani rafi dake Isaka, ta jihar Port Harcourt.
Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar sa ne a saman ruwa bayan kwananki biyu da bada sanarwar cewa ya sullube a daga cikin kwale kwale akan hanyarsa ta komawa kauyen da yake bautar kasa.
Sauran abokan da suke bautar kasar tare da matashin sun bayyana bakinciki da kaduwar su akan rasa abokin nasu.
Daga karshe sun bayyana cewa matashin ya je wani kauye ne domin yin aski, wanda a hanyarsa ta komawa gida ya zame daga cikin kwale kwale inda ya fada cikin ruwan wanda yayi sanadiyyar rayuwarsa.