'Yan Sanda Sun Bankado Makerar Bindigogi A Jihar Benue

A jiya talata ne Jami’an ‘yan sanda a jihar Benue suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da makerar bindiga wadda ba kan ka’ida ba.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar PPRO Moses Yamu, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Makodi, cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar ne suka damke mutanen su biyu.

Jami’in ya kara da cewa an cafke mutanen ne a yayin da ‘yan sandan ke gudanar da ayyukan binciken ababen hawa akan hanya yayin da suka kama mutanen da wata karamar bindiga kirar gida tare da su.

Ya kuma bayyana cewa bincike akan kamun ya kaiga gano wata makerar bindigogin a kauyen Tsar, dake yankin karamar hukumar Vandieka dake jihar Benue. Jami’in ya bayyana cewa an gano nau’ukan bindigogi da dama kirar gida a makerar.

Daga karshe ya bayyana cewa an gano wani akwati makare da kayayyakin kera bindigogi da kuma harsasai duk a cikin akwatin. Jami’in ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar zata yi aiki tukuru domin kawo karshen kera wa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba a daukacin jihar ta Benue