Dan Najeriya Da Lashe Kyautar Sarauniyar Ingila!

Imrana Alhaji Buba

Imrana Alhaji Buba, dan asalin karamar hukumar Jakusko ne a Jihar Yobe, wanda yake zaune a garin Fataskunm na jihar ta Yobe. Yayi karatu a makarantar Kwata Primary School Fataskunm, da kuma Government Day Secondary School Fataskunm. Bayannan ya samu damar zuwa Jami’ar Maiduguri, inda ya karanci kimiyyar Siyasa (Political Science) wanda ya samu kammala digiri shi na farko da matakin farko (First Class degree).

Bayan kammala karatun shi ya shiga cikin harkar taimaka ma matasa, wajen kokarin fahimtar rayuwa. Ganin yadda matasa da yawa a Arewacin Najeriya, ke shiga kungiyar BokoHaram da sauran kungiyoyin ta’addanci. Hakan yasa Imrana, ya kafa wata kungiyar hadin gwiwar matasa, masu yaki da ta’addanci mai suna (Youth Coalition Against Terrorism).

A shekarar 2010, a yayin da yake karatu a jami’ar Maiduguri. Kungiyar tana gudanar da karantarwa ne akan zaman lafiya, a makarantun sakandare da kuma samar da sana’o’i ga matasa marasa sana’a. Kuma kungiyar tana tallafawa matasan da rigimar Boko Harama ta shafa, wajen basu shawarwari na yadda zasu zama mutane a cikin al’umma.