Taimakon Al'umah Da Kasa, Babu Inda Baze Kai Mutun Ba!

Imrana Alhaji Buba

Imrana Alhaji Buba, dan Najeriya, da ya lashe kyautar Sarauniyar Ingila na matasa shugabanni. Ya samu wannan kyautar ne a irin gudunmawar da yake badawa, a tsakanin matasa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

A dalilin gudumawar da Imrana ke bayarwa wajen kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya, ya karbi kyautar girmamawa a wurin Sarauniyar Ingila (Queen’s Young Leaders Award) da kuma horarwa ta musamman a jami’ar Cambridge. Wannan kyautar girmamawa ana bawa matasa 60, ne a kowa ne shekara a kasashe 54, da ingila ta rena (Commonwealth countries).

Sannan an zabe Imrana a cikin shirin horar da matasa masu kawo zaman lafiya (Generation Change Fellows Program) wanda hukumar samar da zaman lafiya ta Amurka (United States Institute of Peace) take gudanarwa, da kuma shirin horar da shuwagabannin matasa (Young African Leaders Initiative) wanda shugaban kasar Amurka Barack Obama ya assasa.

Shawarar Imrana ga matasa shine su nemi ilimi na addini da na boko. Sannan su nemi sana’anr yi. A cewarsa rashin ilimi da sana’a shi yake cusawa matasa mugayen dabi’u, wanda ya kesa su shiga kungiyoyin ta’addanci.