Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka , mai shekaru arba'in da takwas “Celine Dion” na shirye-shiryen daukar hutun da zata zauna tare da ‘ya’yanta, tun dai bayan rasuwar mijinta a farkon wannan shekarar. Mawakiyar tashi ga cikin halin damuwa na rashin mijinta Mr. Rene Angelil.
Mijin nata yamutu ya barta da ‘ya’ya biyu 2, Rene-Charles mai shekaru goma sha biyar 15, sai ‘yan tagwayen su Eddy da Nelson, masu shekaru shida da haihuwa 6. Jaridar “People Magazin” ta ruwaito cewar mawakiyar na neman lokaci da zata nunama ‘yayan ta kauna wanda tun bayan rasuwar mahaifin su, basu samu lokacin ta ba.
Yanzu babban burinta shine, ta bama ‘ya'yan nata kulawa ta musamman, don ganin suna cikin koshin lafiya, ta fadi cewar irin halin da tasa kanta ba zai dawo mata da mijin nata ba, don haka gara ta dawo da rayuwar ta inda ya kamata, shine a kan yaran ta.
Mawakiyar ta bayyanar da wata dabi’a da yaran kanyi aduk rana, sai su dinga sunbantar marikin kofa, da tunanin ko mahaifin su zai dawo. Su kan kuma aika da rubutun sako a jikin balan-balan ga mijin nata. Yanzu babban kokari na shine na nuna ma ‘ya'ya na cewar ni tsayyyar mace ce, inji mawakiyar Celine.