'Yan Najeriya Na Bada Gudun Mawa, Mai Yawa Wajen Cigaban Duniya!

Shamsudeen Musa

Shamsuddeen Musa, haifaffen anguwar Sarki a birnin Kaduna ne, haka kuma ya kammala karatun firamari da sakandiren shi duk a garin Kaduna. Bayan nan ya samu damar zuwa jami’ar jihar Gombe. Inda ya fara da karatun share fage “Remedial Studies” na tsawon shekara daya, bayan kammalawa sai ya fara karatun digiri, kana ya samu nasarar kammalawa a shekarar 2011.

Daga nan Shamsuddeen, ya samu damar zuwa bautar kasa, inda ya samu damar sanin makamar aiki a hukumar matatar mai ta kasa a birnin Abuja NNPC. Bayan kammala aikin bautar kasa, ya samu aiki da kamfanin mutane kasar China, mai suna ”Tongyi Allied Mining Limited” a birnin Abuja. Yayi aiki da su na tsawon shekara daya.

Yanzu haka dai Shamsuddeen, yana kasar Ingila, inda yake karatun digiri na biyu, a jami’ar Hull. A bangaren kasuwanci da cigaban kasa. Inda yake kara jawo hankalin matasa, da su mike tsaye wajen ganin sun taimaka ma cigaban kasa, a kowane hali, don basu da abun da za suyi ma kasar su da ya kamata su tashi tsaye wajen gina ta.

Irin gudun mawar 'yan Najeriya, a kasashen duniya baya misaltuwa, don haka yake ganin cewar, matasa da suke a gida Najeriya, su kokarta wajen neman ilimi, da kokarin amfani da shi ta hanyar da ya dace. Don kara daga martaba da darajar kasar a idon duniya.