Rashin Lafiyar Dana Yasa Ni Jigilar Hodar Iblis - Inji Wani Malamin Makaranta

Wani mai koyar da ilimin na’ura mai kwakwalwa, Mr Anukaenyi Bob-Manuel Ogochukwu da jami’an tsaro suka damke dauke da Hodar Iblis, a filin saukar jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Legas, daga Nairobi na kasara Kenya, ya ce ya shigo da ita ne domin dansa mai shekaru hudu da haihuwa na cikin matsanancin halin rashin lafiya.

Matashin ya bayyana haka ne yayin da jami’an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi suka kama shi a filin saukar jirgin sama na Murtala Muhammed dake birnin Legas yayin da yake dawowa gida daga kasar Kenya.

A cewar ofishin hulda da jama’a na jami’an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi Ofoyeju Mitchell, an kama Ogochukwu ne bayan sakamakon zarginsa da shan kayan mayen ya nuna cewa yana dauke da ita, yayi bayan garin kulli sittin da shidda 66 na hodar iblis da ya hadiya, wanda nauyin ta ya kai 1.115kg.

Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa mutumin dan kabilar Igbo, ya bayyanawa jami’an cewa wannan ne karo na farko da ya taba harkar miyagun kwayoyi, kumna yayi hakanne domin ya sami kudin da zai biya magungunan dansa dake fama da rashin lafiya a can kasar ta kenya, wanda likitoci suka ce yana da rami a kahon zuciyarsa.

Da yake amsa tambayoyi, matashin ya bayyana cewa shi malami ne a makrantar koyon na’ura mai kwakwalwa, Onitsha, kuma ya shiga harkar ne saboda ya nemi taimako wurin jama’a da dama amma babu wanda ya kula shi da taimakon.

Daga karshe ya bayyana cewa wanda ya aike shi da hodar iblis din dan asalin kasar Tanzaniya ne yayi masa alkawari kudi dalar Amurka 2000, ya ce yana ciin matsananciyar damuwa akan rashin lafiyar dan nasa.