Kowa Na Iya Zama Likitan Cutar Sankarau

A yan kwanakin nan ne dai aka samu bulluwar cutar sankarau, a wasu sassan jihohin Arewancin Najeriya, a jihohi kamar su Zamfara, Sakkwato da ma jihara Kano, hakan yasa DandalinVOA, duba muhimancin hanyoyin magance yaduwar cutar Sankarau.

Mun karbi bakoncin wasu iyaye mata domin jin hanyoyin kare kai, daga wannan annoba, musamman akan yara.

Malama Aisha Muhammad, ta ce a wannan lokaci tana barin tagogin a bude, bata bari yara suna kwana da kaya, sannan sai ta tabbata cewar yara sunyi wankan dare.

Ita kuwa Malama Falmata Kachalla, cewa tayi a wannan yanayi, a matsayinta na uwa, barcinta kalilan ne, domin tana yawan tashi da daddare akai-akai domin tabbatar da cewar suna barci, an canza musu makwanci da zarar ta fuskanci sun jike da gumi.

A wannan yanayi bayan wankan dare, tana tabbatar da an shafa musu hoda, bata cunkushe su a daki daya, sannan tana yawan duba su a cikin dare.