Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Facebook – Na Biyu

Facebook

Yadda Zaka Toshe Sakonnin Dake Cika Maka Akwati Cewa Ka Buga Wannan Wasa Ko Wancan

Masu amfani da shafin zumunci na Facebook su kan rika ganin sakonni masu bata rai a wasu lokuta, wai daga abokai ne suna son mutum ya buga wannan wasa ko wancan a wayarsa. Kamar mutum yana da lokacin da zai bata wajen yin wasanni, ko games, a koyaushe.

To akwai hanyar da mutum zai iya bi domin murkushe irin wadannan sakonnin, ba zai sake ganinsu ba.

  1. Idan wayarkja ta Android ce, kuma kana amfani da APP na Facebooka kan Android, sai ka bude shi. Idan ka bude sai ka taba alamar wurin karin bayani ko MORE, watau wasu layuka uku daya a kasa da daya ajere a can sama a gefen dama. Wannan zai bude SETTINGS. Idan wayarka iPhone ce, wannan alama ta MORE tana kasa a gefen dama.
  2. A APP na Android, sai a sauko kasa a a zabi APP SETTINGS. A wayar iPhone kuma, sai a sauko kasa a zabi SETTINGS sannan a zabi ACCOUNT SETTINGS.
  3. Daga nan sai a matsa NOTIFICATIONS. A Android, akwai wata alama mai janyuwa, watau SLIDER a jikin APPLICATION REQUESTS, sai a matsa a ja ta zuwa inda aka sanya OFF, watau an kashe ke nan. Idan kana amfani da wayar iPhone ce, sai ka matsa NOTIFICATIONS, ka zabi MOBILE sai ka matsa ka cire alamun ✓dake gefen APPLICATION REQUESTS da APPLICATION NOTIFICATIONS.

Idan kayi haka, ba zaka sake ganin irin wadannan sakonni masu bata rai ba.

A kashinmu na uku nag aba, zamu fada muku yadda mutum zai raba Facebook dinsa da ma duk wani APP, domin ya huta ma ransa, ba tare da ya rufe shafinsa na Facebook din ba.

Saurari cikakken bayanin;