A shirin mu na mata, yau dandali ya zanta da wasu samari da 'yan mata inda suka yi mana bayani akan yadda suke bayyana ra'ayin su musamman idan suka ga wadanda suke so. Mun fara tattaunawar ne da 'yan mata inda budurwa ta fari ta ce;
"A gaskiya idan na ga saurayin da nake kauna, ko ban fada mashi ba, ni zan san yadda zan jawo shi a jika har ya gane cewar lallai ina son shi. Idan kuma mai mata ne, zan rika jan dansa a jiki ina bashi kyaututtuka da sauran abubuwa makamantan su, idan bashi da mata kuma, kanen shi zan fara neman jawo wa a jiki, idan kuma akwai shakuwa tsakanin mu to zan iya fada mai."
Mai magana ta biyu kuma cewa ta yi, kawai abinda take yi shine yawaita dariya da murmushi da zarar sun yi ido hudu da juna. Ta kara da cewar koda magana ya ke da wasu, zata rika yawan shiga maganar sa, ta ce uwa uba ma idan ta gamu da shi a hanya har wani taku take canzawa.
Wata kuma cewa ta yi yawaita kwalliya da zata ja hankalin saurayi ba wata abu mai wuya ba ce, ta kara da cewa ita a nata ra'ayin bazata iya bude baki har ta fada ma saurayin tana son shi ba domin akwai kunya.
Da muka waiwayi samari kuma, wani matashi ya bayyana mana cewar lallai lamarin yakan sa ya fara ba budurwar kyauta da haka har zai jawo hankalin ta.
Ga karin bayani;