Abubuwan Da Ake Haifar Mutane Dasu Basu Yawa

Mutane a wurin da bom ya fashe a Kano, 24 ga Yuli 2014.

A cikin nazarce nazarcen rayuwa da ake a harkokin ilimi, abubuwan da ake harfar mutum dasu basu yawa, haka kuma abubuwa marasa kyau da ake haifar mutum dasu kalilan ne.

Bisa ga irin tarbiyar da mutum ya taso da ita alokacin dayake matakin da za’a bashi tarbiyar daya kamata a bashi. Matsala irin ta sa ido dai wata aba ce da mutane ke koya a wurin mutanen da suke mu’amula dasu, ta hanyoyin zamantakewa. Kasancewar sa ido ‘dabi’a ce da mutum ke dauka a hanyoyin da yake bi wajen wanzar da rayuwar sa.

Sa ido dai ya rarrabu kashi kashi, idan aka duba za’a ga cewar wasu mutane na da sa ido dayawa, wasu kuma ‘dan kadan ne, har akwai mutanen da za’a gani cewar sa idon nasu ‘kalilan ne. A cikin ire iren wadannan matakan akwai wasu da zarar sun sa ido zasu iya haifar da wata futuna ta hanyar sa idon da suka yi.

Sa ido dai ‘dabi’a ce ta wasu mutane, wadda ka iya harfar da hassada acikin zukatansu, kowanne mutum kan iya sa ido akan mu’amala ta wani ko ta wata da ta shafeshi kokuma bata shafeshiba, amma ba kowa ake sawa ido ba, hakan nada wahala a samu wani bil adam da baya yin irin wannan halayya ta sa ido, koda kuwa kalilan ne za’a ga cewa ana samu. Ana iya ganewa ga wasu wanda keyi dayawa wasu kuma bama a iya ganewa, haka mutane na amfani da abin da suka gani a wajen sa idon domin yin amfani da shi a harkokin rayuwar su ko kuma su haddasa wani abu.

Sa ido dai wani abu ne mai kyau idan har mutane na amfani da shi ta hanyar da yakamata, domin tana nuna yadda mutane zasu sa ido kan abubuwan da suke faruwa domin kawo gyara da tabbatarwa da anyi abubuwan da suka kamata.