A ci gaban rahoton dandalin VOA game da siyasa da sauran al'amuran yau da kullum, mun samo wani Almajirin Allo mai suna Isa Idris wanda yasa wayarwa da ‘yan uwansa almajirai kai don ganin sun yi siyasa ba da gaba ba kamar yadda ya yiwa Wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir bayani.
Yace, “Ina son in ga cewa na wayar da kan abokan huldata don in tabbatar ba su shiga hayaniya ba. Kowa ya bar dan uwansa ya zabi wanda yake so a siyasa domin abu ne na ra’ayi”.
Data tambaye shi maganar sayar da katin zaben dindindin da wasu ke yi sai yace mata su a cikinsu sun kai su 40 sannan jam’iyyarsu daya kuma wajen sana’arsu daya. Ya nuna mata cewa wasu da zasu sayr amma ya wayar musu da kai cewa lallai in suka saida katin zabensu to hakika sun saida ‘yancinsu.
Ya kuma tabbatar mana cewa ya shawo kansu, domin a cikin su 40 din nan da suke tare guda 3 ne kawai suka dage kan cewa za su iya sayarwa. Sai dai yace ya fada musu in har suka saida to shi ba ruwansa da su kowa ya kama gabansa kawai.
Daga karshe yayi kira ga almajirai ‘yan uwansa da suka isa kada kuri’a da cewa su jajirce su tafi ranar zaben su kada kuri’a ba tare da wani tashin hankali ba.