An Bukaci Daliban Kasar Sudan Da Ke Karatu Zimbabwe Su San Inda Dare Ya Yi Masu

An umurci daliban kasar Sudan ta kudu da aka tura karatu babban cibiyar nazarin harkokin kimiyya da kere-kere da ke Zimbabwe, da su tattara ya nasu ya nasu su san inda dare yayi musu, domin gwamnatin kasarsu ta kasa biyan kudin makaranta.

Daliban su 29, sun ce hukumar makarantar ta umurce su da su bar makarantar tun sati guda da ya shige, domin gwamanatin kasar su ta gaza biyan dubban dalolin kudin makaranta da na kwana har na tsawon zangon karatu Uku.

A cikin wasikar da makarantar ta rubuta, wadda Muryar Amurka, ta samu ganin abinda aka rubuta ciki, makarantar tace tana bin daliban kudi dalar Amurka, dubu dari biyu da 41, da dari 894.

Gwamnatin ta Sudan ta kudu ta gaza cimma wa’adin lokacin da makarantar ta bata na karshen watan da ya gabata, domin biyan wadannan kudaden.

Daliban suka ce rashin biyan wadannan kudaden ya tilasta su barin cikin makarantar su koma Ofishin jakadancin kasarsu dake Harare, kuma sun roki gwamnbatin kasar da tayi kokari ta biya wadannan kudaden don su samu damar komawa bakin karatunsu.

Haka kuma daliban sun koka cewa ko a ofishin jakadancin da suke da zama suna zama a takure ne, domin ba su samun wadataccen abinci da wurin kwana, da wurin kewayawa.

Giir Salfa Deng, dan shekaru 25, daya daga cikin daliban da ke shekara ta biyu a matakin karatu a makarantar, ya ce kwas din da yake yi, kasar tasa na matukar bukatarsa.