An Cafke Matashiyar Da Ta Kashe Dala Miliyan Uku Kan Jakkunan Hannu

Jami'an 'yan sandarn kasar Australia sun kama wata yarinya mai shekaru 21 da haihuwa da laifin aikata zamba a yayin da ta yi ikirarin cewar ta kashe kudin da wani banki ya saka a asusun ajiyar ta bisa kuskure dalar Amurka miliyan 3.4, kwatankwacin Naira miliyan dari tara da talatin wajan sayen jakunan hannu.

Rahotanni sun bayyana cewa matashiyar mai suna Christine Jiaxin Lee, wadda daliba ce a bangaren koyon aikin kere kere ta yi ta canza wuraren zama masu kayan alatu da kuma jakunan hannu masu tsadar gaske da sauran kayayyakin kwalliya masu tsada.

Bankin kasar ne yayi kuskuren saka wadannan makudan kudi a asusun ajiyar wannan matashiya, yayin da ita kuma ta ci gaba da kisan kudin kamar yadda taga dama musamman wajan sayen jakkunan hannu.

"Turkashi, lallai kin tara jakkuna da yawa kuma masu tsada" a cewar mai shari'a Lisa Stapleton kamar yadda wata kasida ta wallafa a kasar.

'Yan sanda sun cafke matashiyar ne jiya laraba da daddare a yayin da take kokarin shigajirgin sama domin sulalewa zuwa kasar Malaysia, rahotanni sun ce an tuhume ta da laifin aikata rashin gaskiya da zamba a yayin da bankin ya yi kuskuren saka kudi dalar Amurka miliyan 4.6 cikin asusun ajiyar ta.

Lee ta kashe wadannan kudade ne a tsakanin watan Yulin shekarar 2014 zuwa watan Afirilun shekarar 2015. yanzu haka dai an bada belin ta kuma kotu zata cigaba da sauraren karar a ranar 21 ga watan Yunin wannan shekarar.